A sakon ta'aziyyar, Xi ya ce, ya yi matukar kaduwa da samun labarin mummunan harin wanda ya hallaka mutane masu yawa.
A madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin da kuma shi kansa shugaba Xi, yana nuna juyayi game da hasarar rayukan da aka samu a kasar Somaliya, kana yana jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata a harin.
A kalla mutane 276 ne harin ya hallaka, wasu mutanen sama da 300 kuma sauka jikkata a harin bom din wanda ya faru a ranar Asabar a wasu rukunin shaguna a Mogadishu, an bayyana harin da cewa shi ne mafi muni da aka taba samu a tarihin hare-haren da ake kaddamarwa a kasar ta Somaliya. (Ahmad Fagam)