Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau cewa, gwamnatin kasar Indiya ta sha bayyana ra'ayinta na amincewa da yarjejeniyar iyakar ta da lardin Xizang na kasar Sin, wanda tuni aka rattaba hannu kan hakan tun a shekarar 1980.
MR. Geng ya ce muddin an daddale irin wannan yarjejeniya ta iyakar kasa da kasa, to ko shakka babu sauyin gwamnati ko tsarin mulkin kasa, ba zai yi tasiri ga halascin yarjejeniyar da kuma aikinta ba. (Kande Gao)