Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Col. Onyema Nwachukwu ya fitar a jiya Juma'a, ta ce an mika mutanen ne ga Gwamnatin jihar a cibiyar gyaran hali dake Unguwar Bulunkutu a Maiduguri babban birnin jihar.
Col. Onyema Nwachukwu ya ce an kama mutanen ne yayin aikin da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole ke yi a yankin arewa maso gabashin kasar da nufin murkushe 'yan tada kayar baya, ya na mai cewa an kuma sallami mutanen ne bayan hadaddiyar cibiyar samar da bayanan sirri ta rundunar wato JIC, ta gudanar da bincike tare da yi musu tambayoyi.
Kakakin ya kara da cewa, Kwamadan cibiyar Brig-Janar Abdulrahman Kuliya ne ya mika mutanen ga Gwamnatin jihar.
Ya kuma yi kira ga al'umma su bada hadin kai tare da bada bayanai masu amfani ga hukumomin tsaro kan duk wani abu da ba su yarda da shi ba a yankunansu. (Fa'iza Mustapha)