Da yake jawabi yayin wani taro a birnin Fatakwal mai arzikin man fetur, babban hafsan sojin saman kasar Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce rundunar sojin ta yi nasarar wanzar da zaman lafiya tare da tsare yankin arewa maso gabashin kasar daga ayyukan Boko Haram.
Air Marshal Abubakar, ya alakanta nasarorin da aka samu da farmaki ta sama da kasa da a ka kai kan tungar mayakan Boko Haram, tare kuma da kokarin sauran hukumomin tsaro.
Har ila yau, Babban hafsan sojin saman, ya ce rundunar sojin ta samu dimbin nasarori a yankin arewa maso gabas da sauran yankunan kasar tun bayan da sabuwar gwamnati ta kama aiki a shekarar 2015. (Fa'iza Mustapha)