in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma sakamako mai kyau a taron sauyin yanayi na Bonn
2017-11-19 13:41:56 cri
A safiyar ranar 18 ga watan nan da muke ciki ne, aka rufe taro kan sauyin yanayi na Bonn na MDD, a maimakon ranar 17 ga wata da aka tsara tun da farko.

Bisa shawarwarin da aka yi a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa, an cimma sakamako mai kyau a yayin taron, lamarin da zai ba da gudummawa sosai wajen kammala shawarwari kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Paris a kan lokaci.

Cikin wannan taron da aka yi a birnin Bonn na tarayyar Jamus, an zartas da kudurori da dama da suka hada da shirin gudanarwa ta Fiji da dai sauransu. Haka kuma, an tsara wani daftarin yin shawarwari mai kiyaye daidaituwa a tsakanin bangarori daban daban wanda Yarjajeniyar Paris ta shafa, inda aka tabbatar da matsaya kan yadda za a gudanar da taron shawarwari na shekarar 2018, yayin tsara jadawalin gaggauta ayyukan kiyaye yanayin duniya kafin shekarar 2020. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China