Guterres ya ce, a 'yan shekarun nan, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannonin da suka shafi raya tattalin arziki, muhalli da yanayi, wadda ta kasance babbar aminiyar MDD. A bana, shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi a gun taron dandalin tattaunawa na Davos gami da hedikwatar MDD dake birnin Geneva, inda ya jaddada cewa, kasar Sin za ta martaba yarjejeiyar Paris, kana, rahoton da aka fitar a wajen babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya ce, kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta wajen neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, al'amarin da ya samu yabo matuka daga MDD.
A nasa bangaren, Xie Zhenhua ya ce, yana fatan MDD za ta kara fadakar da kasashe daban-daban kan alakar kut da kut dake tsakanin tinkarar sauyin yanayi da burin neman ci gaba mai dorewa nan da shekara ta 2030, a wani mataki na raya harkokin duniya ba tare da gurbata muhalli ba kuma cikin dogon lokaci. (Murtala Zhang)