Jiya Laraba ta kasance ranar Afirka a yayin babban taron sauyin yanayi dake gudana a birnin Bonn. Cibiyar nazarin harkokin ci gaba ta kasar Jamus gami da cibiyar bada shawarwari kan harkokin Sin da Afirka mai hedikwata a birnin Kӧln na Jamus, sun shirya wannan taron karawa juna sani, inda wakilan gwamnatocin Sin da Jamus da Afirka, gami da na wasu cibiyoyi da kungiyoyin kasa da kasa suka tattaunawa kan yadda za su fadada hadin-gwiwa a fannin tinkarar matsalar sauyin yanayi da neman ci gaba mai dorewa.
Kasar Jamus ta dade tana taimakawa kasar Sin tinkarar matsalar sauyin yanayi, kana, tana samar da dimbin taimako ga kasashen Afirka a fannin raya makamashin da ake iya sabuntawa. Ita kuma kasar Sin, ta jima tana kokarin raya amfani da makamashin da ake iya sabuntawa a nahiyar Afirka. Saboda haka, inganta hadin-gwiwa tsakanin wadannan bangarori uku, wato Sin da Jamus da Afirka, zai kara kokarin da ake na bunkasa makamashin da ake iya sabuntawa a kasashen Afirka, da neman ci gaba a wasu sauran fannoni da dama. (Murtala Zhang)