in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a aiwatar da Yarjejeniyar Paris yadda ya kamata
2017-11-16 15:03:18 cri
A wajen taron sauyin yanayi da Majalisar Dinkin Duniya ta kira a birnin Bonn na kasar Jamus, kasashen dake tasowa gami da masu hannu da shuni sun yi sa-in-sa dangane da matakan da za'a dauka, domin tinkarar sauyin yanayi kafin shekara ta 2020.

A ganin tawagar kasar Sin, muhimmin abun da za'a yi domin warware sabanin ra'ayi tsakanin kasashe daban-daban shi ne, kara fahimta gami da aiwatar da Yarjejeniyar Paris yadda ya kamata.

A gun taron, kasashen dake tasowa da dama, ciki har da kasar Sin, wakilan kasashen sun yi kira da a tsara wani jadawali, game da matakan da za'a dauka, domin tinkarar matsalar sauyin yanayi a fadin duniya kafin shekara ta 2020. Wani wakili daga tawagar kasar Sin, kana, jami'i daga sashin kula da yanayi na kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin, Mista Chen Zhihua ya ce, matakan da za'a dauka sun hada da, gaggauta aiwatar da gyararren shirin Doha na Yarjejeniyar Kyoto kan tinkarar sauyin yanayi, da kuma sa kaimi ga kasashe masu sukuni don su tabbatar da cimma burin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli kafin shekara ta 2020, da sauke nauyin dake wuyansu na tallafawa kasashen dake tasowa a fannin fasaha da kudi.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban tawagar kasar Sin, kana wakili na musamman kan harkokin tinkarar sauyin yanayi na gwamnatin kasar, Xie Zhenhua ya ce, babban sabanin ra'ayin dake tsakanin kasashe masu tasowa da kuma kasashe masu sukuni shi ne, batun ko akwai bambanci tsakanin matakan da za su dauka domin tinkarar sauyin yanayi ko kuma babu. A ganin Xie, na farko, ya kamata bangarori daban-daban su kara fahimta gami da aiwatar da Yarjejeniyar Paris yadda ya kamata. Na biyu, a kara samun amincewar siyasa tsakanin juna. Na uku shi ne, a daidaita alaka tsakanin tinkarar sauyin yanayi da raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma, ta yadda za a iya neman samun ci gaba cikin daidaito. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China