Da yake karin haske kan lamarin, minista a ofishin harkokin sadarwa na gwamnatin Habasha Negeri Lencho ya bayyana cewa, gwamnati ta kafa wata rundunar soja don taimakawa wadanda fadan ya rutsa da su.
Ya kara da cewa, duk da fadan da ya barke a jiya a kan iyakar Oromia da jihar Somali, har yanzu al'amura na tafiya yadda ya kamata a yankin.
Bayanai na nuna cewa, jihohin Oromia da Somali sun shafe kusan shekaru 20 suna fama da rikicin kan iyaka.
Ko da a makon da ya gabata sai da wani kazamin fada ya barke a kan iyakar Oromia da Somali, lamarin da ya rikide zuwa fadan kabilanci, inda har mutane da dama suka mutu kana dubban jama'a suka bar muhallansu.(Ibrahim)