in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ciyar da shawarwarin neman sulhu na Syria gaba, in ji manzon musamman na MDD
2016-04-23 13:03:40 cri
Jiya Jumma'a 22 ga wata, manzon musamman na MDD kan batun Syria Staffan de Mistura ya bayyana cewa, ko da yake, kwamitin kula da harkokin yin shawarwari na babbar jam'iyyar adawa ta Syria ya dakatar da halartar taron shawarwarin neman sulhu dake gudana a halin yanzu, amma, zai ci gaba da dukufa wajen ciyar da shawarwarin neman sulhu gaba, inda zai kuma tabbatar da gudanarwar shawarwarin har zuwa ranar 27 ga wata, ta hanyoyin yin shawarwari na kai tsaye da kuma ba na kai tsaye ba.

Kaza lika, ya ce, za a kawo karshen shawarwari a ran 27 ga wata, sa'an nan, zai ci gaba da neman taimako da goyon baya na gamayyar kasa da kasa, domin kira taron ministocin waje na mambobin kungiyar goyon bayan Syria ta kasa da kasa, da kuma ciyar da ayyukan da abin ya shafa gaba yadda ya kamata.

Ban da haka kuma, bisa labarin da aka samu a ran 22 ga wata, an ce, wakilan gwamnatin kasar Syria da wakilan kungiyar dakaru ta Kurds sun yi ganawa a birnin Damascus na kasar, inda suka tattauna kan yadda za a iya kawo karshen rikice-rikice a birnin Kameshli dake arewa maso gabashin kasar Syria. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China