in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kasance a kan gaba wajen raya sha'anin kudi ba tare da gurbata muhalli ba, in ji MDD
2017-11-17 13:43:59 cri
Jiya Alhamis, hukumar kiyaye muhalli ta MDD wato UNEP ta fidda wani rahoto mai taken "bayani kan ci gaba kasar Sin wajen bullo da tsarin harkokin kudi ba tare da gurbata muhalli ba", inda ta bayyana cewa, raya sha'anin harkokin kudi bisa ka'idojin kare muhalli zai taimakawa kasar Sin a matakan da take dauka na yin kwaskwarima a fannonin tattalin arziki da zaman takewar al'umma. Haka kuma, ana ganin cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana kan gaba a wannan fanni, ta kuma samu sakamako da dama a fannonin aiwatar da manufofin da abin ya shafa, da kuma zama jagora ga kasashen duniya.

Rahoton ya kuma kara da cewa, a shekarar 2016, kasar Sin ta yi nasarar shigar da batun raya sha'anin harkokin kudi ba tare da gurbata muhalli ba cikin taron kungiyar G20, sa'an nan, gwamnatin kasar ta tsara tare da ba da shawarwari kan yadda za a inganta wannan aiki.

Bayanai na cewa a halin yanzu, kasar Sin ta kasance abin koyi ga kasashen duniya kan yadda za a raya kasuwannin samar da takardun bashi tare da kiyaye muhalli yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China