in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na adawa da matakin Koriya ta arewa na karya kudurin MDD
2017-09-15 19:36:27 cri
Da sanyin safiyar yau Jumm'a ne kasar Koriya ta arewa, ta harba wani makami mai linzami zuwa yankin teku dake kudu maso gabashin yankin Koriya. Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta nemi kowane bangaren da wannan lamari ya shafa, da ya kai zuciya nesa, tare da kaucewa daukar matakan da ka iya tsananta halin da ake ciki a yankin Koriya da na shiyya-shiyya.

A nata bangare, kasar Amurka ta yi kira ga kasashen Sin da Rasha, da su matsa wa kasar Koriya ta arewa lamba a wannan lokaci. Game da wannan kira, madam Hua Chunying ta ce, matsalar mafi tsanani game da batun nukiliyar Koriya ita ce, sabanin dake tsakanin kasashen Koriya ta arewa da Amurka. Don haka kamata ya yi bangarorin da abun ya shafa, su dage wajen sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata.

A yayin taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kan shirya na rana rana a yau Jumm'a, madam Hua Chunying ta ce, al'ummomin duniya suna tsayawa kan matsayin tabbatar da ganin an warware batun nukiliyar yankin Koriya ta hanyar siyasa da diflomasiyya. A waje daya, karin mutane na ganin cewa, saka takunkumi ba zai warware matsalar daga asali ba. Abun da ya fi muhimmanci da kuma ya kamata kowane bangare ya yi ba tare da bata lokaci ba shi ne, dakatar da dukkan matakai ko kalamai, wadanda za su tsananta halin da ake ciki.

Har ila yau, ya kamata kowane bangare ya yi namijin kokari, na daukar matakan a zo a gani, game da yadda za a aiwatar da kudurin MDD daga dukkan fannoni cikin daidaito, ta yadda za a iya kafa yanayi na neman dabaru masu dacewa, ta warware matsalar da ake fuskanta ta hanyar tattaunawa cikin ruwan sanyi. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China