in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da tsohon shugaban Laos
2017-11-14 10:41:18 cri

Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping wanda ke ziyarar aiki a kasar Laos, ya gana da tsohon shugaban kasar, kuma tsohon babban sakataren jam'iyyar juyin juya hali ta kasar, ko LPRP a takaice Choummaly Saygnasone.

Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya jinjinawa irin gagarumar gudummawa da Mr. Choummaly ya bayar cikin shekaru 10 da suka gabata, a fannin bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Laos, da karfafa kawance na gargajiya dake tsakanin kasashen biyu, da ma hadin gwiwar sassan daga dukkanin fannoni, a lokacin da yake rike da ragamar jam'iyyar dake mulkin kasar ta Laos.

A nasa bangare, Mr. Choummaly taya kasar Sin murna ya yi, game da kammala babban taron wakilan JKS karo 19 cikin nasara, musamman ma sanya tunanin shugaba Xi Jinping cikin kundin tsarin mulkin jam'iyyar, game da tsarin mulkin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China