in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Laos sun lashi takobin karfafa danganta mai cike da alfanu ga juna
2017-11-14 09:47:41 cri

Kasashen Sin da Laos sun bayyana kudurin su, na kafa wani tsari da zai ba su damar bunkasa hadin gwiwa mai cike da alfanu ga juna a nan gaba.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, da shugaban kasar Laos, kuma babban sakataren jam'iyyar juyin juya hali ta kasar, ko LPRP a takaice Bounnhang Vorachit ne suka tabbatar da hakan, yayin ziyarar aiki da shugaba Xi ya gudanar a kasar ta Laos.

Shugabannin biyu dai sun jinjinawa juna, game da kyakkyawar dangantakar dake wanzuwa a tsakanin su, sun kuma amince da daukar matakan bunkasa musaya a fannin al'adu, da samar da horo.

Hakan dai na zuwa ne yayin da kasar Sin ke dada kaimi, wajen gudanar da sauye sauye, da kara bude kofa ga kasashen waje. A gabar da ita ma kasar Laos ke aiwatar da gyaran fuska a manufofin ta, tare da sauya tsarin tafiyar da kasa.

Shugabannin biyu sun kuma tabbatar da kudurin su, na ci gaba da martaba makwaftaka, da kawance mai daraja, da abokantaka ta gargajiya, da hadin gwiwa. Kaza lika suna fatan hakan zai daga matsayin dangantakar su zuwa wani sabon matsayi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China