Karamin ministan kula da sufurin jiragen saman kasar Hadi Sirika da ya bayyana haka a jiya, ya ce za a sa hannu kan yarjejeniyar ne a cikin mako mai zuwa a Abuja, babban birnin kasar.
Hadi Sirika, ya ce kamfanin Airbus na kasar Fransa ma ya nuna sha'awarsa na hadda hannu da gwamnatin Nijeriya wajen kafa kamfanin kula da yin gyara da kuma yi wa jiragen sama garambawul a kasar.
Ministan ya ce kudurin gwamnatin na kafa kamfanin jiragen sama da na kula da gyara jiragen, yunkuri ne na sake fasalin bangaren sufurin jiragen saman.
Tuni gwamnatin ta sanar da nada masu bada shawarwari game da kafa kamfanonin. (Fa'iza Mustapha)