Da yake jawabi yayin kaddamar da wani littafi a Abuja, babban birnin kasar a jiya Alhamis, Muhammadu Buhari ya ce, yana son ya ba al'ummar kasar tabbacin kudurinsa na inganta tsaro da yaki da cin hanci da sake fasalin tsarin tattalin arziki.
Gwamnatin Buhari dai na daidai tsakiyar wa'adinta, inda littafin mai shafuka 360 ya tabo nasarori da gwamnatin ta samu a fannonin siyasa da zaman takewa da ci gaban tattalin arziki.
Muhammadu Buhari, ya shaidawa mahalarta taron cewa, yakin da ake da cin hanci ya fara samun kyawawan sakamako.
Har ila yau, ya ce kasar za ta iya biyan basusukan da ake binta. Yana mai cewa, darajar takardar lamunin kasar na kasashen waje ya zarce kima.
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin magance rikicin makiyaya da manoma da yaki ci yaki cinyewa da matsalar satar mutane dan neman kudin fansa da kuma fashi da makami. (Fa'iza Musatpha)