in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Najeriya sun jinjinawa Super Eagles game da nasarar da ta samu kan Argentina
2017-11-16 10:01:32 cri
Masu sha'awar wasannin kwallon kafa a Najeriya sun yabawa babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Super Eagles, sakamakon kokarin da suka yi a wasan da suka buga inda suka yi galaba kan kungiyar wasan Albiceleste ta kasar Argentina a wasannin sada zumunta na kasa da kasa da aka buga a Krasnodar, na kasar Rasha.

Super Eagles ta yi nasara ne kan Albiceleste da ci 4-2 a wasan da suka buga.

Da yake mai da martani game da wasan a Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya, Ifeanyi Udeze, tsohon mai tsaron bayan kungiyar ta Super Eagles, ya ce tawagar 'yan wasan sun nuna kwazo kuma sun taka rawar gani a wasan da suka buga da takwararsu ta kudancin Amurka.

Haka zalika, Festus Allen, tsohon kociyan kungiyar wasan kwallon kafan 3SC FC ta Ibadan ya ce, wannan nasara ta kasance kara kaimi ne ga kungiyar wasan ta Super Eagles. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China