Abbas Aliyu, mataimakin darakta ne a ma'aikatar lafiya ta jihar ya shedawa 'yan jaridu a jihar Sokokto cewa, an ga alamun ciwon kai mai tsanani a jikin wasu mutane 3, da jijjiga kuma jini yana fita daga idanunsu.
Binciken farko da likitoci suka gudanar ya nuna cewa, ana zargin cutar maleriya ce ta haddasa mutuwar mutanen.
Sai dai ya ce, ya yi matukar nadama sakamakon rashin daukar samfurin kwayoyin cutar daga jikin mutanen da suka mutu wadanda tuni an riga an binne su tun a ranar da suka mutu, ya kara da cewa, kawo yanzu ba'a kara samun rahoton wani mutum da ya kamu da cutar ba.
Daraktan ya ce, an samu makamancin wannan al'amari a shekarar da ta gabata kuma an yi wa wadanda suka kamu da cutar magani ne a matsayin wadanda suka kamu da kwayoyin cuta dake sa zazzabi mai zafi, wanda yake da matukar bukatar kulawa ta musamman. (Ahmad Fagam)