in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu abubuwan fashewa sun halaka mutane 18 a Najeriya
2017-11-16 19:00:49 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 18 ne suka gamu da ajalinsu ciki har da 'yan kunar bakin waken,bayan da suka tayar da abubuwan fashewar dake jikinsu a garin Maiduguri a yankin arewa maso gabashin kasar, kana cibiyar mayakan Boko Haram.

Mai Magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Borno Victor Isuku ya shaidawa manema labarai cewa, wasu 'yan kunar bakin wake hudu ne suka kutsa cikin wani masallaci dake Muna garaje, a kusa da garin na Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda suka tayar da abubuwan fashewar dake jikinsu, suka kashe kansu da kuma wasu mutane 14 dake Ibada a wurin. Lamarin dai ya faru ne jiya da misalin karfe 8:15 na maraice agogon wurin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China