in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hatsarin jirgin kasa ya yi sanadin mutuwar mutane 3 a Nijeriya
2017-11-17 09:34:46 cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane uku sanadiyyar wani hatsarin jirgin kasa da ya auku da safiyar jiya Alhamis a jihar Lagos dake zaman cibiyar harkokin kasuwancin kasar.

Rundunar ta ce jirgin ya ci karo ne da wata katuwar mota dake tafiya a yankin Agege na jihar, inda mutane da dama suka raunana.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Olarinde Famous-Cole, ya ce jami'an tsaro da masu aikin ceto sun isa wurin don kai dauki.

Ya kara da cewa, ana gudanar da bincike don tantance musababbin hatsarin da kuma jimilar mutanen da ya rutsa da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China