Rear Admiral Suleiman Apochi, shi ne kwamandan rundunar tabbatar da tsaro ta (JTF), dake aiki a jihar Delta, ya ziyarci yankin Enekorogha a ranar Laraba inda aka yi garkuwa da 'yan kasar Birtaniyan su 4, kuma daga bisa guda daga cikinsu ya rasa ransa.
Kwamandan ya bayyana yin garkuwa da 'yan kasar wajen dake aiki a Najeriyar a matsayin zubar da kimar kasar, don haka ya bukaci al'ummar yankin da su taimakawa hukumomin tsaro don su samu damar zakulo bata gari a yankin.
Mutanen 4 'yan Birtaniya suna gudanar da aikin bada tallafin kiwon lafiyar ga al'ummar yankin ne a kyauta, kuma an yi garkuwa da su ne tun a ranar 13 ga watan Oktoba. Guda daga cikinsu ya rasu a hannun masu garkuwar, yayin da ragowar ukun suka kubuta daga hannun masu garkuwar bayan wasu makonni. (Ahmad Fagam)