Babban hafsan sojojin ruwa na kasar Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Calabar dake kudancin kasar. Ya ce babu wata kungiya da ta isa ta hargitsa zaman lafiya da hadin kan Najeriya.
Kungiyar tsagerun yankin wato Niger Delta Avengers a kwanan nan ta sanar da aniyarta na sake ci gaba da lalata kayan aikin hako danyan mai a yankin, tana mai cewa gwamnatin kasar ta gaza cika alkawarin da ta dauka na daidaita al'amurra a yankin.
A shekarar bara, haren-haren da mayakan tsagaren yankin suka kaddamar ya yi sanadiyyar rage adadin man da kasar ke samarwa wanda ba'a taba samun irinsa ba cikin shekaru 20 da suka gabata, lamarin da ya haifarwa kasar rasa matsayinta na kasar dake kan gaba mafi samar da danyen mai a nahiyar Afrika.
Hafsan sojin ruwan ya ce, dakarun sojojin ruwan kasar a shirye suke su yi fito na fito da mayakan dake yi wa yankin mai azrikin mai barazana.
Ya kara da cewa dakarun sojin kasar a shirye suke su tunkari duk wata kungiyar dake neman tada hargitsi ko wargaza zaman lafiyar kasar. A shirye suke su dakile duk wani yunkuri na gurgunta ci gaban tattalin arzikin kasar. (Ahmad Fagam)