Da yake amsa tambayoyin wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, bayan gabatar da wata makala game da yaki da ta'addanci, da kare hakkokin bil'adama a jami'ar London, Mr. Guterres ya bukaci Sin ta ci gaba da wannan muhimmin aiki da take gudanarwa. Ya ce akwai matukar bukatar kasashen duniya su dage, wajen hadin gwiwa da juna a fannin yaki da ta'addanci, wanda a cewarsa muhimmancin hakan ya sa a badi, zai kira taron shugabannin hukumomin yaki da ayyukan ta'addanci irinsa na farko karkashin inuwar MDD, domin fadada hadin kai wajen gina tsari, na tallafawa juna da amincewa juna a fannin.
Babban magatakardar MDDr ya kuma bukaci kasashe mambobin majalissar, da su himmatu wajen ganin sun dakike hanyoyin da 'yan ta'adda ke bi, wajen samarwa kungiyoyin su kudade, da bunkasa musaya a fannin tsaro.
Ya ce a shekarar da ta gabata kadai, an samu aukuwar hare-haren ta'addanci har 11,000 a kasashe sama da 100. Yana mai kashedin cewa hakan barazana ce ga zaman lafiya, da tsaro, da ma ci gaban daukacin kasashen duniya. (Saminu Hassan)