in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Benin sun shiga tawagar yaki da Boko Haram
2017-11-17 08:49:24 cri
Dakarun sojin kasar Benin su 150 sun shiga rundunar sojojin hadin gwiwa dake yaki da kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi. A cewar kakakin rundunar hadin gwiwar kanar Mustapha Anka, wadannan sojoji na kasar Benin sun kunshi mayaka 142, da kuma hafsoshi 8.

Kanar Anka ya ce tuni sojojin suka isa helkwatar rundunar dake sansanin Farcha dake birnin Ndjamena, fadar mulkin kasar Chadi.

Yanzu haka dai Benin ce kasa ta 5 da ta aike da sojojinta cikin wannan runduna, wadda ke da dakaru daga kasashen Najeriya da Nijar, da Kamaru da Chadi. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China