in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana ayyukan gona na kasar Sin sun bude wani shirin bada horo a Jamhuriyar Benin
2017-08-04 09:38:18 cri
Masana ayyukan gona na kasar Sin, sun fara wani shirin bada horo na kwanaki 10, ga manoma da masu kiwo da malaman gona na Jamhuriyar Benin.

An shirya taron ne bisa hadin gwiwar ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin da cibiyar koyar da dabarun noma ta kasar Sin dake Benin da ma'aikatar harkokin gona da kiwon dabbobi ta Jamhuriyar Benin.

Wakilin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Wang Rui, ya ce horon zai ba mahalartansa damar koyon dukkan tsare-tsaren noma na kasar Sin domin kara yada dabarun noma musammam noman masara da kayayyakin lambu da ma kiwon kaji masu yin kwai.

Har ila yau, Wang Rui ya ce dabarun noman da za a koyar za su ba manoman Benin damar samun karin kudaden shiga tare da bunkasa harkokin gona.

A nasa bangaren, babban jami'in sashen ayyukan da koyar da sana'o'i na ma'aikatar harkokin gona ta Benin Leopold Biaou, yabawa ya yi da fasahohin noma irin na kasar Sin, yana mai cewa, an gwada fasahohin noman masara da kayayyakin lambu na kasar Sin a Benin, al'amarin da ya sa aka samu karin yawan masara da ake nomawa daga ton 1 a kowanne hekta zuwa sama da ton biyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China