in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta kaddamar da bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa
2017-01-10 10:07:44 cri
Jamhuriyar Benin ta kaddamar da bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa karo na 8 a birnin kasuwancin kasar Cotonou.

Mr. Ange N'Koue, ministan raya al'adu da yawon bude ido na jamhuriyar Benin, da Jakadan Sin a jamhuriyar Benin, Diao Mingsheng, sun halarci bikin, wanda aka gudanar a karshen mako a babban dakin taro na cibiyar raya al'adu ta kasar Sin dake Cotonou.

Wani Basine mai yin zane zane, da kuma wasu 'yan Afrika 3, sun tsara wasu tufafi na musamman wadanda aka yi amfani da su don yin fareti a lokacin bikin. Mutanen su ne; Xu Ming daga kasar Sin, Sonia Tohon daga Benin, Joseph Adebayo daga Najeriya, da kuma Gilles Comlan daga Togo.

Patrick Idohou, shi ne manajan shirya bikin, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, bikin bazara na Sinawa a Benin zai kunshi jerin bukukuwa da dama da suka hada da bikin baje koli, da bikin haska fitilu, da faretin nuna al'adun gargajiya, da shirya gasar haska fitilu na Sinawa.

Da yake gabatar da jawabi a yayin kaddamar da bikin, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Benin, Diao Mingsheng ya ce, bikin sabuwar shekarar Sinawa ta bana wato shekarar kaza, za'a fara ne daga ranar 28 ga watan Janairu, kuma za ta kasance shekarar yin musayar bayanai domin samun dankon zumunta tsakanin al'ummar Sinawa da jama'ar kasar Benin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China