in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jamhuriyar Benin na sa ran zama cibiyar samar da fasahar zamani a yankin yammacin Afrika kawo shekarar 2021
2017-05-18 09:54:31 cri
Gwamnatin Jamhuriyar Benin na shirin mai da kasar wata cibiya ta samar da fasahar zamani ga yammacin Afrika kawo shekarar 2021.

Ministar fasaha da sadarwa ta kasar Mrs Rafiatu Monrou ce ta bayyana haka cikin wata sanarwar da aka fitar a jiya Laraba domin bikin ranar sadarwar wayar tarho da yada bayanai ta duniya da aka yi a jiyan.

Mrs Monrou, ta ce ta yi imanin cewa, taken bikin na jiya "manyan bayanai domin kyakkyawan tasiri"ya dace da manufar Shugaban kasar Patrice Talon na bukasa tattalin arzikin bangaren fasahar zamani.

Ta ce tsarin na da nufin sauya Jamhuriyar Benin zuwa cibiyar samar da hidimomin fasahar zamani da gaggauta samar da ci gaba da kuma samarwa al'umma dammamaki cikin shirin ya zuwa shekarar 2021.

Ta kuma jadadda muhimmnacin tabbatar da samun hidimomin intanet kan farashi mai rahusa a fadin kasar, da kuma daukar matakai daki-daki na kafa wata cibiyar kasa ta harkokin sadarwa, wadda za ta share fagen shimfida babbar wayar ta Fibre Optic da tsayin ta zai kai sama da kilomita 3000 nan da shekarar 2019 mai zuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China