Jami'in mai suna Jose Pliya, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen 2, zai daga matsayin harkar yawon shakatawa a Benin. Ya ce kasar na da dama ta cin gajiya mai gwabi daga harkar yawon bude ido, to sai dai kuma ba a maida kai sosai wajen cin gajiyarsu ba.
Mr. Pliya na wannan tsokaci ne a gefen taron kasa da kasa game da harkar yawon bude ido da aka bude a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Rwanda.
An dai bude taron na yini 4 ne a ranar Litinin, da nufin bunkasa harkar yawon shakatawa, harkar dake zama jigo ga bunkasar tattalin arziki, da samar da guraben ayyukan yi a daukacin sassan nahiyar Afirka.