in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Philippines sun amince za su karfafa kyakkyawar mu'amala a tsakaninsu
2017-11-16 10:43:37 cri
A jiya Laraba kasashen Sin da Philippines suka rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa 14 a yayin da shugabannin kasashen biyu suka yi alkawarin zurfafa kyakkyawan hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

Bayan wata ganawar da ta gudana tsakanin shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte, da firaiministan kasar Sin Li Keqiang, wanda ke ziyarar aiki a kasar, sun shedawa 'yan jaridu a Manila babban birnin kasar ta Philippines cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da da Philippines ta inganta kuma dukkanin bangarorin suna fatar yin aiki tare da juna domin cike gibin da suka fuskanta a baya.

A nasa bangaren, Duterte, ya godewa kasar Sin saboda irin taimakon da take baiwa kasar ta Philippines wajen sake gina yankin Marawi, da kuma irin taimakon da Sin take baiwa Philippines wajen gina kasa da gina kayayyakin more rayuwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China