Da yake jagorantar taron kasar Sin da kungiyar ASEAN karo na 20 a Manila tare da Shugabn Philippine Rodrigo Duterte, Li Keqiang ya ce burin zai daukaka tsare-tsaren hadin gwiwar kasar Sin da ASEAN zuwa wani sabon mataki ta yadda dangantakar za ta taba kowanne bangare yayin da za ta maida hankali ga batutuwa 3 da suka hada da tabbatar tsarin siyasa da tattalin arziki da cinikayya da kuma musaya tsakanin al'ummominsu.
Li Keqiang ya ce har kullum, kasar Sin na ba dangantakarta da ASEAN muhimmanci a harkar diflomasiyyar makotaka, kuma kudurinta ne daukar ASEAN a matsayin aminiya kuma makociya ta kwarai, da za su yi aiki tare wajen shawo kan kalubale da kuma samar da al'umma mai kyakkyawar mako da akidu da manufofi na bai daya. (Fa'iza Mustapha)