in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron shugabannin kungiyar ASEAN da na kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu a birnin Manila
2017-11-14 15:54:01 cri
Yau Talata, an yi taron shugabannin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ta ASEAN da na kasashen Sin, Japan da Koriya ta Kudu karo na 20 a birnin Manila, fadar mulkin kasar Philippines.

A yayin taron, shugabannin kasashen sun nuna yabo matuka kan kyawawan sakamakon da aka cimma cikin shekaru 20 da suka gabata, inda suke kuma sa ran ci gaba da kiyaye zaman lafiya da huldar abokantaka dake tsakaninsu, ta yadda za a samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa.

Shugaban kungiyar ASEAN ta wannan karo, watau shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte, shi ne ya jagoranci taron, kana firaministan kasar Sin Li Keqiang, da takwaransa na kasar Japan Shinzo Abe, da kuma shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in na cikin mahalarta taron.

A yayin taron, an tattauna kan yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kungiyar ASEAN da kasashen uku a nan gaba, inda aka kuma yi musayar ra'ayoyi game da harkokin zuba jari, da cinikayya, da kiyaye muhalli, da kuma neman dauwamammen ci gaba da dai sauransu.

A yayin dake ba da jawabi, Mr. Duterte ya ce, cikin shekaru 20 da suka gabata, hadin gwiwar dake tsakanin kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan da kuma Koriya ta Kudu tana ci gaba da bunkasuwa. Kuma, an cimma nasarori da dama, bisa fatan su na neman bunkasuwa cikin hadin gwiwa. Ya ce a nan gaba kuma, ya kamata a ci gaba da yi hadin gwiwa domin neman ci gaba tare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China