in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin: kasar Sin da EU na bukatar shawo kan matsalolinsu bisa hangen nesa
2017-11-15 10:08:28 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kamata ya yi kasar Sin da Tarayyar Turai EU, su yi kokarin warware dadaddiyar matsalar dake tsakaninsu bisa hangen nesa.

Li Keqiang na wannan tsokaci ne lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar EU Donald Tusk, a wani bangare na jerin taron shugabannin kan hadin gwiwar gabashin Asia a birnin Manila na Philippines.

Firaministan ya bukaci EU ta sauke nauyin dake kanta karkashin kuduri na 15 na yarjejeniyar kasar Sin da hukumar kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO, ta yadda za a tabbatar da duk wata doka ta dace da ka'idojin hukumar. Ya kuma yi kira ga EU ta nuna goyon baya ga tsarin cinikayya mai 'yanci tare da saukaka hanyoyin zuba jari.

A cewar kudurin na 15 kamata ya yi a ce kasashe mambobin WTO su daina fakewa da tsarin tsawwala haraji kan kasar Sin wajen dakile sayar da kayayyaki masu arha tun ranar 11 ga watan Disamban bara. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China