Firaministan na Sin ya ce kawo yanzu, ba a kai ga warware matsalolin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta ba, baya ga kalubalen da rashin tabbas a fannin ke haifarwa, akwai kuma batutuwa na tsaron yankuna, ciki hadda barazanar ta'addanci dake kara bazuwa.
Ya ce a irin wannan yanayi, abu ne mai wahala a cimma daidaito, da wadatar tattalin arziki ko dunkulewar yankin gabashin Asiya wuri guda, don haka ya zama wajibi a yabawa dukkanin ci gaba da aka samu ko min kankantarsa.
Da ya tabo batun nasarar kammalar taron wakilan JKS karo na 19 da aka gudanar cikin watan jiya a nan birnin Beijing, Mr. Li ya ce taron ya amince da ci gaba da bin hanyoyin lumana wajen samar da ci gaba, da dada sabunta alakar kasa da kasa tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, tare da gina al'ummar duniya dake da burin cimma moriyar juna.
Ya ce ci gaban kasar Sin zai haifar da damammaki na bunkasar kasashen dake yankin na gabashin Asiya, da ma sauran sassa na duniya baki daya, ba kuma zai haifar da wata barazana ga wani bangare ba. (Saminu Hassan)