in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin kayayyakin kide-kide da aka sayar a kasar Sin a bana zai haura dala biliyan 6
2017-10-14 12:29:23 cri
Kungiyar masu sayar da kayayyakin kide-kide ta kasar Sin ta bayyana cewa, a bana an sayar da kayayyakin kide-kide da kudinsa ya haura dala biliyan 6.1.

An samu wannan ci gaba ne a 'yan shekarun nan, biyo bayan yadda yaran Sinawa ke yawan sayan kayayyakin kide-kide, musamman yada wadanda ke zaune a manyan biranen kasar ke sha'awar shiga darussan koyan kida.

Kungiyar masu sayar da kayayyakin kide-kiden ta ce a watanni shida na farkon wannan shekara, masu kera kayayyakin kide-kide 253 wadanda kudaden shiga da suke samu ya dara Yuan miliyan 20 a kowace shekara, sun samu cinikin da ya kai na Yuan biliyan 19.

Alkaluma na nuna cewa, yawan kudaden da suka samu daga cinikin da suka yi a shekara ya kai Yuan biliyan 24.5.

Bugu da kari, kungiyar ta bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara, kayayyakin kide-kide da ake fitarwa zuwa kasashen ketare ya ragu, amma yawan wadanda ake shigo da su ya karu da kaso 6.9 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, tun bayan ga gwamnati ta rage harajin da ake karba kan kayayyakin kide-kiden da ake shiga da su cikin kasar.

Yanzu haka akwai sama da hukumomin koyar da kide-kide 640,000 a kasar Sin, yayin da darajar cibiyoyin horas da kide-kide ta haura Yuan biliyan 70 a shekarar da ta gabata. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China