in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufofin tsarin tattallin arzikin Nijeriya za su rage hadduran dake tattare da karbar bashi
2017-11-04 12:44:02 cri
Ministar kudin Nijeriya Kemi Adeosun, ta ce manufofin kula da harkokin da suka shafi basussuka da kudaden shiga na kasar, za su rage hadurran dake tattare da karbar rance tare da gaggauta raya kasa.

Wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya Jumma'a a birnin Lagos cibiyar harkokin kasuwanci na kasar, ta yi maraba da shawarar asusun lamuni na duniya IMF dangane da matakin kasar na karbar karin rance daga ketare.

Ministar ta ce kara karbar rance daga ketare zai taimaka wajen samar da kudaden shiga yayin da zai rage nauyin bashi dake kan kasar ta hanyar tsawaita lokacin biya.

Kemi Adeosun ta kara da cewa, rance daga ketare zai kara yawan kudin asusun ajiyar kasar na ketare, da magance raguwar zuba jari daga bangarori masu zaman kansu tare da tara kudin biyan rancen.

Ta ce wani muhimmin bangare na manufofin sake fasalin tsarin tattalin arzikin kasar shi ne, tattara kudaden shiga domin inganta daidaito tsakanin basussukan da ake bin kasar da kuma kudaden shigarta.

A cewarta, an dauki wannan mataki ne ta hanyar wasu dabaru, ciki har da toshe duk inda ke da baraka da kuma amfani da fasahohin wajen tattara kudaden shiga. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China