Buratai wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai yau Talata, ya ce dakarun da aka tura za su gudanar da wannan aiki ne cikin hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi da kewaye, domin gano da kuma kawar da ragowar gyauron mayakan na Boko Haran dake barna a yankunan dake kan iyakokin kasashen da ke makwabtaka da Najeriya. (Ibrahim Yaya)