Cibiyar samar da makamashi ta kasar Rasha wato Rosatom ta sanar a ranar Litinin cewa, an cimma yarjejeniyar ne a lokacin taron ministocin kasashen duniya game da amfani da makamashin nukiliya marar illa wanda aka gudanar a Abu Dhabi, babban birnin hadaddiyar daular larabawa, inda aka nazarci matakan da za'a bi wajen amfani da kimiyyar makamashin nukilya don samar da zaman lafiya.
Anton Moskvin, mataimakin shugaban hukumar samar da makamashi ta Rusatom ya bayyana cewa, wannan wani babban aiki ne mai matukar muhimmanci, wanda zai kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci.
Mista Moskvin ya bayyana cikin sanarwar cewa, cigaban fasahar nukiliya zai baiwa Najeriya damar daukaka matsayinta na zama babbar jagora a nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)