Biyu daga cikin sabbin ministocin ba su halarci wajen ba, amma ana sa ran rantsar da su a wani lokaci nan gaba.
Ministocin da suka sha rantsuwar kama aikin su ne tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri Happyton Bonyongwe, wanda aka nada a matsayin ministan shara'a, wanda ya karbi aiki daga hannun mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa, sauran su ne ministan ci gaban matasa, da ministan hukumar kula da 'yan kasa da samar da ayyukan yi Chiratidzo Mabuwa, da Edger Mbwembwe, a matsayin sabon ministan yawon bude ido.
Mabuwa shi ne tsohon mataimakin ministan ciniki da masana'antu, yayin da Mbwembwe ya kasance mataimakin ministan harkokin waje.
Gyaran fuskar da shugaba Mugabe ya yi wa majalisar ministocin kasar ya shafi ministoci 10 ne, inda ya nada sabbin ministoci 8 kana ya sauke ministoci 3. (Ahmad Fagam)