in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na nuna gamsuwa da dukkan matakan dake taimakawa kokarin warware batun nukiliya a yankin Koriya
2017-09-14 19:08:11 cri
A yayin taron manema labaru na rana rana da aka saba shiryawa, a yau Alhamis, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta bayyana cewa bangaren Sin na nuna gamsuwa, da dukkan matakai, da za su tallafawa kokarin warware batun nukiliya a yankin Koriya cikin ruwan sanyi, da wadanda aka dauka domin farfado da shawarwarin sulhu tsakanin bangarori daban daban.

Haka kuma, bangaren Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa, za su yi amfani da damar da ake da ita, su kuma hammantu a fannin siyasa, tare da dora muhimmanci kan hakan ba tare da wani bata lokaci ba.

Rahotanni na cewa, a jiya Laraba, mai magana da yawun majalisar gudanarwar kasar Amurka madam Heather Nauert, ta ce, har yanzu, daidaita batun nukiliya na Koriya ta hanyar diflomasiyya, ya kasance zabi na farko ga bangaren Amurka. Kaza lika a dai wannan rana, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayar da wata sanarwar, inda ta ce, daidaita batun nukiliya a yankin Koriya a siyasance ta hanyar diflomasiyya, shi ne mataki daya tilo a gaban kowane bangare.

Bugu da kari, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce ya kamata kowane bangare ya yi namijin kokarin samar da yanayin da zai taimaka wajen warware batun nukiliyar Koriya a siyasance, kuma ta hanyar diflomasiyya.

Game da hakan, madam Hua Chunying ta ce, al'ummomin duniya suna tsayawa kan matsayin tabbatar da ganin an raba yankin Koriya da sinadarin nukiliya, da kuma warware batun nukiliya na yankin Koriya ta hanyar siyasa da diflomasiyya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China