Dan kasar Lebanon Hussein Awada, ya zama zakara a rukunin maza, wanda ya zo a matsayi na 9. Nisrine Njiem shine ya jagoranci tawagar 'yan wasan Lebanon rukunin mata da matsayi na 10.
Uwar gidan shugaban Lebanon Nadia Aoun ta shiga gasar gudun mita 8 a wasannin share fage na gasar.
Jakadan kasar Australiya a Lebanon Glenn Miles, shine cikakken jakada a wasan na gudun yada kanin wani, yayin da jakadan Burtaniya Hugo Shorter ya kasance daga cikin jami'an diplomasiyya da suka shiga gasar gudun mita 21.
Tun daga lokacin da aka fara gasar wasannin gudun yada kanin wani a shekarar 2003, kimanin mutane 393,000 ne suka shiga gasar gudun wadan da suka fito daga kasashe da yankuna na duniya 105, kana sama da dala miliyan 1.3 ne aka samu a gasarnin. Masu shirya gasar na shekarar 2017 sun bayyana cewa, a kalla mahalarta 45,000 ne suka halarci wasannin, wadan da suka yi nasara daga rukunin maza da mata kowannensu ya samu kyautar kudi dala 10,000. A wannan shekarar sama da ma'aikatan sakai 4,400 ne suka bada taimako wajen gudanar da harkokin wasannin.(Ahmad Fagam)