in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jinjinawa 'yan wasan tseren kasar Kenya
2016-03-16 13:41:01 cri
Jami'an dake kula da harkokin wasanni da masu horas da 'yan wasan tseren kasar Kenya, sun jinjinawa 'yan wasan kasar da suka halarci gasar gudun dogon zango ko "Africa Cross Country Championships" da aka kammala ranar Asabar a birnin Yaounden kasar Kamaru.

A cewar shugaban hukumar wasannin kasar wato AK, Mr. Jack Tuwei, 'yan wasan Kenya sun nuna bajimta, sun kuma cimma nasarori ba tare da amfani da kwayoyin kara kuzari ba, duk kuwa da kallon da ake yiwa kasar na kin daukar kwararan matakan dakile wannan halayya yadda ya kamata.

Mr. Tuwei ya kara da cewa 'yan wasan Kenyan ne ke mamaye gasar, tun fara gudanar da ita a shekara ta 2010, lokacin da aka fafata a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu. Baya ga nasarar 'yan wasan na Kenya a wannan karo, Tuwei ya ce akwai alamu dake nuna za su ci gaba da taka rawar gani a gasar Olympics ta Rio dake tafe da ma sauran gasanni na kasa da kasa.

A nasa bangare babban kocin 'yan wasan Julius Kirwa, cewa yayi juriya da kwarewa da 'yan wasan suka nuna yayin da suke karbar horo a birnin Yaounde, zai taimaka musu matuka wajen samun nasarori a gasar Olympics dake tafe.

Kenya dai ita ce ke kan gaba a gasar ta bana, wadda ita ce irin ta ta 4 da aka gudanar, inda 'yan tseren ta suka lashe lambobin girmamawa da aka sanya, in ban da kasashe biyu da su ma suka samu lambobin yabo a gasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China