A kwanan baya ne dai aka ayyana wasan tseren na Guangzhou a matsayin wanda ya yi fice, wanda hakan ya shaida cewa, wasan Marathon na birnin Guangzhou ya riga ya zama muhimmin wasan a kasar Sin.
A kwanakin bayan ne dai a nan birnin Beijing, aka gabatar da jerin sunayen manyan wasannin Marathon na kasar Sin na shekarar 2017 zuwa 2018, inda wasan Marathon na Guangzhou, da na Beijing, da na Chongqing, da na Wuhan, suka zama wasannin dake sahun gaba ake gudanar a kasar Sin.
An dai tabbatar da cewa, gasar manyan wasannin Marathon ta kasar Sin da hukumar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ta kafa, take kuma gudanarwa, na daya daga cikin manyan wasannin Marathon mafi kayatarwa a kasar Sin. Burin kafa su kuwa shi ne kyautata tsarin gudanar da wasan Marathon na kasar Sin, da kafa ma'aunin gudanar da irin wannan wasan a kasar, da sa kaimi wajen gudanar da wasan da zai kai matsayin kada da kasa, da bin ka'idoji mafiya dacewa, da yanayin kasuwa, da yada al'adu da tunanin wasanni, da kafa dandalin yin mu'amala, da kuma zama misali na sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin wasan a kasar Sin.
Bayan da aka fara gudanar da wasan Marathon na birnin Guangzhou a shekarar 2012, an koyi fasahohi da tunani na sauran wasannin Marathon dake gudana a sauran sassa na ciki da waje, da gudanar da wasan bisa ma'aunin kungiyar hadin gwiwa ta guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya. Kana an zabi wasan a matsayin wanda ya kasance mai kayatarwa a kasar Sin a shekaru 3 a jere.(Zainab)