Yayin gasar wadda ita ce karo na 43, Bekele ya kai matsayin bajimta na biyu da aka taba kafawa, amma bai kai ga cimma matsayin da Dennis Kimetto ya kafa ba, inda ya gaza hakan da dakikoki 6 kacal.
Daya daga cikin 'yan tseren da ya taba samun nasarar lashe gasar ta birnin Berlin wato Wilson Kipsang, a wannan karo y agama gudun sa ne a matsayi na biyu, da dakikoki 10 bayan Bekele. Yayin da shi ma Evans Chebet ya gama gudun sa cikin sa'oi 2 da mintuna 5 da dakikoki 31.
Da yake tsokaci game da nasarar da ya samu, Bekele ya ce ya so kafa wani tarihi na kashin kan sa, sai dai bai samu zarafin yin hakan ba. Burin sa shi ne na kafa wani sabon matsayi na bajimta.
A bangaren mata ma 'yan kasar Habashan ne suka mamaye gasar, inda Aberu Kebede ta gama tseren cikin sa'oi 2, da mintuna 20, da dakika 45, yayin da Birhane Dibaba ke biye da ita a matsayi na biyu (2:23:58), sai Ruti Aga (2:24:41). (Saminu Alhassan)