Kimutai wanda yayi nasarar tserewa Cherono da Korir bayan gudun kilomita 40. cikin sa'oi biyu, a gudun mintoci 6 da dakika 4, ya isa shi kadai ne a kan titin Coolsingel inda ya kammala. Cherono ya isa da misalin (2:06:21) kuma ya kammala karo na biyu saia Korir daya kammala da misalin (2:06:25) wanda aka kammala a filin wasan kasar Kenya.
Meskerem Assefa daga kasar Habasha itace ta samu nasara a rukunin mata. Ta samu nasarane bayan da tserewa Eunice Chumba daga kasar Kenya a wasan kilomita na karshe, inda tayi gudun kilomita cikin sa'oi 2:24:18. Chumba ta isa cikin dakika 9, bayan da yar wasan kasar Kenya Lucy Karimi ta kammala cikin sa'oi (2:25:17) ta kammala zagaye na 3.(Ahmad Fagam)