Wani jami'in rundunar sojin ta hudu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun dake goyon bayan gwamnati, sun tunkari gabar ruwa ta Mocha, inda suka kwace iko da sassan dake yankin, bayan wani kazamin fada.
Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kawo yanzu, ana ta gwabza fada a yankin, kuma dakarun za su ci gaba da tunkarar tekun Mocha.
Majiyoyi daga jami'an kiwon lafiya na cewa, sama da mayakan Houthi hamsin da sojojin kawance goma sha tara ne suka rasa rayakansu yayin fadan.
Jiragen yakin rundunar kawance da Saudiyya ke jagoranta sun taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa sojojin kwace yankunan gaabar ruwan yammacin Yemen da kuma hanyar ruwa ta Bab Al Mandab. ( Fa'iza Mustapha )