Hukumar ta ce wutar lantarki da ake amfani da shi ya karu zuwa kaso 7.2 a kan na shekara daya da ta gabata, inda ya karu a kan kaso 6.4 na watan Augustan da ya gabata.
Ta kara da cewa, cikin watanni 9 farkon shekarar nan, an yi amfani da jimilar kilowatts trillion 4.7, wanda ya karu da kaso 6.9 a kan na makamancin lokacin a bara.
Yawan lantarki da aka yi amfani da shi a bangaren harkokin gona ya karu da kashi 7.8 inda bangaren bada hidima ya karu da kaso 10.5, yayin da bangaren masana'antu ya karu da kaso 6 a cikin wadancan watanni.
Wannan bayani ya nuna cewa alkaluman yawan kayayyakin da masana'antu ke sayarwa ya kai maki 52.4 a watan Satumba, mataki mafi koli da ya kai cikin sama da shekaru 5, a kuma cikin watanni 14 a jere da bangaren ke samun tagomashi.
Tattalin arziki kuma ya fadada da kaso 6.9 cikin rabin farkon shekarar nan idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. A makon gobe ne kuma za a fitar da alkaluman tattalin arziki na GDP na rubu'i na uku na bana. (Fa'iza Mustapha)