Masu nazarin kimiyya da fasaha dake cikin jirgin na "Xiang-yang-hong 01" suna da shirin nazarin labarin kasa, da halittu, da gudanar ruwan teku, da yanayin tekun, da tarkacen ledojin dake cikin teku a kudancin yankin tekun Atlantic.
Wannan ziyara ta zagaya duniya da wani jirgin ruwan kasar Sin ya yi a karon farko, ta shafi nazarin da za a gudanar cikin teku da kuma yankuna masu tsananin sanyi na Antarctic da North Pole.
Jirgin ruwan na "Xiang-yang-hong 01" ya fara ziyararsa ne daga birnin Tsingdao na kasar Sin a ranar 28 ga watan Augustan bana. Ana kuma sa ran ganin dawowarsa zuwa Tsingdao din a ranar 15 ga watan Mayun shekara mai zuwa.(Bello Wang)