Babban jami'in bincike na hukumar lura da tekuna ta kasar Sin (SOA) Li Tiegang, ya ce binciken wanda zai mai da hankali kan albarkatu da muhalli da kuma yanayi a matakai 6, zai gudana ne a rabin ban kasa ta yanki kudu.
A mataki na 4, jirgin zai hadu da jirgin Xuelong na kasar Sin mai shiga cikin kankara dan samar da hanya ga sauran jiragen ruwa, a aiki karo na 34 da yake yi a Antarctika.
Mataimakin darakta a hukumar SOA Lin Shanqing, ya ce tafiyar na da muhimmanci ga kasar Sin wajen gano hanyoyin ci gaba ta fuskar kimiyya tare da kara tasirin da kasar ke da shi a bangaren binciken teku.
Jirgin Xiangyanghong 01 da ya tashi daga Qingdao na gabashin Sin, zai shafe mil 35,000 cikin teku a aikin da zai yi na kwanaki 260, inda aka shirya dawowarsa Qindao a ranar 15 ga watan Mayun 2018. (Fa'iza Mustapha)