Rahotanni sun bayyana cewa, kumbunan biyu sun fara rabuwa ne da karfe 3:29 na yammaci bisa umarnin hakan daga doron kasa, suka kuma kammala rabuwa da karfe 4:15 na yamma. Kaza lika bayan kammala rabuwar kumbunan biyu, Tianzhou-1 ya fara kewaye kan falaki dake da nisan kusan kilomita 400 daga doron kasa.
Kwararru na kasar Sin sun bayyana cewa, kumbon Tianzhou-1 zai ci gaba da ayyukan bincike a falakinsa, musamman a fannin gini da sarrafa tashar sama jannati.
An harba Tianzhou-1 ne a ranar 20 ga watan Afrilun da ya gabata daga tashar harba kumbuna dake lardin Hainan, ya kuma kammala hadewa da kumbon Tiangong-2 a ranar 22 ga watan Afirilu.
Bugu da kari, kumbunan biyu sun kammala sabunta makamashi a ranar 27 ga watan Afrilu, da kuma 15 ga wata Yuni, kafin gudanar da hakan a ranar Asabar din da ta gabata.
Cikin watanni 5 da suka gabata, kumbon Tianzhou-1 na ci gaba da gudanar da ayyukan sa cikin nasara, kamar dai yadda masana a fannin suka tabbatar. (Saminu Hassan)