Yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci kan dangantakar hadin gwiwa da aka kulla a tsakaninta da kasashe daban daban na duniya, kuma a ko da yaushe tana bin hanyar samun ci gaba cikin lumana. Bugu da kari, Sin da kasashe daban daban za su girmama wa juna, da nuna daidaito ga juna, da hadin gwiwa don moriyar juna, domin raya makomar bil Adam ta bai daya.
Baya ga wannan kuma, Li ya nuna cewa, a cikin shekaru kusan 40 da suka gabata bayan da kasar Sin ta kaddamar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, Sin ta samu manyan nasarori a fannonin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kuma kawowa jama'arta alheri, ita ma ta bayar da babbar gudummawa ga zaman lafiya da bunkasuwar duniya baki daya. Kasar Sin na da aniyar hada shawararta ta "Ziri Daya da Hanya Daya" da shirye-shiryen neman bunkasuwa na kasa da kasa domin samun damammakin ci gaba a nan gaba.
A nasu bangaren, jakadun sun bayyana cewa, a matsayinsu na jakadun kasa da kasa da ke kasar Sin, akwai babban nauyin da ke bisa wuyansu, wadanda za su yi kokari don ciyar da dangantaka da ke tsakaninsu da Sin gaba, da ma amfanawa kasashensu jama'arsu.(Kande Gao)